Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

YANZU-YANZU: Ƴan Ta'adda Sun Tarwatsa Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Abuja Da Fasinjoji 970

Labarin dake shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun dasa bom a titin jir...


Labarin dake shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun dasa bom a titin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, inda suka dakatar da shi.

Majiyarmu ta labarta mana cewa lamarin ya faru ne a tsakanin garin Katari zuwa Rijana a daren yau Litinin. 

Daya daga cikin fasinjojin wanda ya shaida lamarin ya ce: 'yan bindigar sun kuma zagaye jirgin inda suka bude wuta na kan mai uwa da wabi. 

Daya daga cikin wanda suka san adadin fasinjojin dake jirgin, ya labartawa Majiyarmu cewa akwai akalla Fasinjoji 970 a jirgin. 

Cikakken labari na nan tafe.

No comments