Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi kan yadda yakin yakin Rasha a Ukraine ke kokarin jefa duniya a ma...
Sakatare
Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi kan yadda yakin
yakin Rasha a Ukraine ke kokarin jefa duniya a matsalar kamfar abinci saboda
yadda rikicin zai hana noma a sassan duniya.
A
jawabinsa gaban manema labarai a birnin New York, Guterres ya ce duniya za ta
fada halin tsaka mai wuya sanadiyyar guguwar yunwa da tsadar kayakin abinci
sakamakon rikicin na gabashin Turai.
Guterres
ya ce farashin kayakin abinci zai yi tashin da duniya bata taba gani ba matukar
ba a dauki matakan da suka kamata ba inda a yanzu haka kasashe da dama ciki har
da na Afrika suka fara dandana kudarsu.
Akalla
kasashe 45 da suka kunshi wasu a nahiyar Afrika da kuma wasu masu tasowa ne
suka dogara da Rasha da Ukraine wajen shigo da tan tan na alkama kuma 18 daga
cikin sun dogara ne kacokan wajen samun kashi 50 na abincinsu daga kasashen
biyu.
Kasashen
da suka kunshi Yemen da Lebanon da Libya da Sudan da kuma Somalia baya ga
Burkina Faso da Masar da kuma Jamhuriyar Demokuradiyar Congo su ne 'yan gaba
gaba da suka dogara da Ukraine da Rasha wajen samun alkama.
Magatakardar
na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce dole ne mahukunta su mike
tsaye don lalubo hanyoyin warware rikicin na Rasha da Ukraine da nufin ceto
duniya daga bala'in guguwar yunwa.
Kwanaki
20 kenan cif da Rasha ta fara mamaya a Ukraine wanda ya kai ga rasa rayukan
dimbin fararen hula baya ga dubunnan dakaru daga kowannen bangare.
No comments