Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Zaɓen 2023: Atiku Ya Sake Ƙaddamar Da Takararsa A Karo Na 6 A Tsawon Rayuwarsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a babban zaɓe na 2023 mai zuwa a...


Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a babban zaɓe na 2023 mai zuwa a jam’iyyar adawa ta PDP.

Wannan shi ne karo na 6 a rayuwarsa da yake ƙaddamar da neman takarar shugabancin Nijeriya. 

Atiku, wanda ya shafe shekara fiye da 15 da su ka wuce ya na neman shugabancin Nijeriya, ya ce zai mayar da hankali kan ɓangare uku idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Da ya ke jawabi ya yin taron a yau Laraba a Abuja, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zama gada tsakanin mulkin dattijai da na matasa idan ya ci zaɓe a 2023.

“Gwamnatinmu za ta zama kamar gada ce [da za ta haɗa] tsakanin mulkin dattijai da na matasa.”

Ya ci gaba da cewa: “A ƙarƙashin mulkina, zan mayar da hankali kan ɓangare biyar masu muhimmanci; haɗin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da ɓangarorin gwamnatin tarayya gaba da ƙara musu iko.”

No comments