Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Zaɓen 2023: Matasa Ku Farka, Cewar Bashir Sakadaɗi

Honorabul Bashir Sakadaɗi, fitaccen dan siyasa ne a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna baki daya kuma a yanzu shi ne Bab...


Honorabul Bashir Sakadaɗi, fitaccen dan siyasa ne a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna baki daya kuma a yanzu shi ne Babban Daraktan neman kujerar Gwamnan jihar Kaduna a tafiyar dan takarar Gwamnan jihar Kaduna Alhaji Isa Ashiru Kudan a zaben 2023.

Wakilinmu ya samu zantawa da shi game da shawararsa a kan matasa. Ga tattaunawar kamar haka; 

MADOGARA: Ranka shi dade ka zama Uba a Jam'iyyar PDP; yanzu haka ga shi an doshi shekarar 2023 al'amuran siyasa na kara dosowa a daidai wannan lokacin me za ka gayawa al'ummar jihar Kaduna da kasa baki daya musamman matasan karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna har da kasa baki daya? 

BASHIR SAKADAƊI: Alhamdulillah, na gode da wannan dama da aka bani. Kuma gaskiya ne nan da shekara guda in Allah ya yarda a fadin Nijeriya kusan duk shuwagabannin da ya kamata a zaba an zabe su ga wanda Allah ya yi wa tsawancin kwana. Dimokuradiyya dai ta kwashe sama da shekara 20, inda ana cewa jam'iyya kaza ce take shugabanci yanzu kuma wata jam'iyyar su yi. Wata jam'iyya ta kwashe shekara 16, yanzu kuma wata jam'iyyar ta cinye 7 ta shiga ta 8. Saboda haka ina kira ga al'ummar kasa, farko dai idan ana cewa ne a zabi jam'iyya to an kwatanta an gani. In ana cewa ne a zabi mutum an kwatanta an gani. Ina kara jawo hankalin matasan Nijeriya da dukkanin dan Nijeriya mai kuri'a, ya zabawa kanshi abin da zai zame masa alkhairi ba ya zaba ma kanshi abin da zai zame masa abin kuka ba kamar irin halin da muke ciki a yau ya zama mana ba mu da wanda za mu ce ga laifin da aka yi ya share mana hawayenmu. 

Ina kira ga matasa lokacin su ne, su yi kokari su zabi shugabannin da za su taimaka a ceto kasar nan daga cikin irin halin da take ciki. 

MADOGARA: Ranka ya dade da yake da yawa wasu 'yan siyasa sukan yi amfani da matasa don haifar da rigima yayin gudanar da zabuka. Ban sani ba ko ka yi wani hange ko wata shawara da za ka bai wa matasa don magance matsalar irin hakan?

BASHIR SAKADAƊI: Gaskiya ne, abin tambaya a baya matasa aka yi amfani da su, amma yanzu ya kamata mu lura domin in alkawari ne na man fetur zai sauka, to ya saukan? Idan alkawarin zaman lafiya ne to an sami zaman lafiya? Mu a yanzu  mun san darajar matasanmu, 'yan jam'iyyar PDP don haka ne matashi muka dauka don mu tabbatarwa da Nijeriya da matasa cewa mun yi shirin mika masu mulki, mai shekara 25 shi ne shugaban matasan Nijeriya a jam'iyyar PDP. A karamar hukumar Sabon Gari yanzu wanda ke wakiltar majalisa ta dokoki bangaren gundumar Sabon Gari dan shekara 40, wanda ke nema dan gundumar Basawa dan shekara 40 ne, wanda muke sa ran yanzu ya nemi majalisar Tarayya dan shekara 40 ne, saboda haka su yi wa kansu kiyamal laili su zabi kansu da kansu, bisa kyakkyawan zaton abin da aka kasa yin masu su yi wa kansu maganin abin ke nan a yanzu. An wuce lokacin da wani matashi za a bashi wani abin da zai yi maye, ko a ba shi abin da ba zai biya bukatarshi na yau da kullum ba. Wadanda suka gama karatun ba aikin yi matasa ne, wanda suke karatun babu kudin biyan karatun a yanzun matasa ne, yanzun haka kudin da yaro zai biya a zango biyu na karatu shi zai biya a zango daya, maganar sana'a kuwa ba ta, to saboda haka muna kiran matasa da su taimaki kansu su taimaki saura kannensu, su yi zabi na abin da ya fi cancanta da abin da zai taimaki rayuwarsu a nan gaba.

MADOGARA: Honorabul mene ne burinka a yanzu?

Buri na shi ne amanar da aka ba wanda suka gudana a baya a jam'iyya, yanzu muna tare da su muna fatar a sake kwatantawa, a kara goya masu baya don samun nasara a tafiyarmu mai tsafta.

MADOGARA: Mungode. 

BASHIR SAKADAƊI: Nima na gode.

No comments