Ambassada Tuggar Daga Idris Khalid Ana ci gaba da yi wa Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, kiran da ya fito ya amsa ...
Ambassada Tuggar
Daga Idris Khalid
Ana ci gaba da yi wa Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, kiran da ya fito ya amsa bukatar neman kujerar gwamnan jihar Bauchi a yayin babban zaben 2023 da ke tafe a karkashin lemar jam’iyyar APC.
Masoya da magoya bayansa, sun ayyana shi a matsayin wanda zai iya kyautata jihar Bauchi idan ya samu dama, don haka ne suka fito suka nemi da ya amince da bukatar da suka jima suna yi don ceto jihar Bauchi.
Tuggar wanda shine Ambasadan Nijeriya a kasar Jamani, magoya bayansa din sun bayyana cewar irinsa ne jihar take bukata domin yana da gogewa a fannin ciyar da tattalin arziki, nemo hannayen jari da kuma bunkasa koyar da sana’o’in dogaro da kai.
Alhaji Bello Muhammad Tukura, shugaban gidauniyar Ambasada Tuggar shine ya shaida hakan a ganawarsa da ‘yan jarida jiya a Bauchi, yana mai bayyanin cewa, Ambasadan na da kishin jihar a cikin ransa don haka ne ya nemi jama’a da su mara wa Tuggar baya.
Ya ce: “Idan ya ce mana baida ra’ayin tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi gaskiya za mu dauki matakin shari’a domin duk abun da jama’a suka ce ka zo ka yi, muna ganin wannan abun shine zai ceto jihar Bauchi daga wannan kangin da ake ciki.
“Mun sani tattalin arzikinmu kaso 95 ya dogara ne a akan albashi. Albashin nan kuwa wasu da dama basu ma samunshi, wasu na tsawon shekara, wasu watannni; wani in ya samu albashi wannan watan, bai da tabbacin samu a wani watan na gaba, baya ga wannan, in ka duba tattalin arzikin kasar ma baki daya na kara komawa baya.
“Don haka muna son nemo jajirtacce, dan zamani, wanda ke da mu’amala da kasashen duniya da zai zo ya duba ya ga yaya za a yi a ciyar da jihar gaba ba tare da ana fargaba ba,” ya bayyana.
Ya tabbatar da cewa, muddin aka zabi Ambasa Yusuf to tabbas zai cire wa al’ummar jihar Bauchi kitse a wuta, “Mutum da ba gwamna ba ma amma ka ga yadda yake taimakon matasa, matasa, dattajai da kowani rukuni, a kowani lokaci jihar ce a zuciyarsa. A kowani lokaci samar da tallafin dogaro da kai yake yi wa matasa da al’umma.”
“Dalilinmu da ya sanya muke son Ambasada da ya zama gwamna shine, ka san gwamnonin Nijeriya suna da wani karfi a hannunsu, wani lokacin duk kudinka duk hanyoyinka na samo cigaba ba za ka iya kawowa jiharka ba muddin gwamnan wannan lokacin baya sha’awar hakan. Don haka muna da tabbacin Tugga zai ceto jihar Bauhci zai nemo hanyoyin bunkasa tattalin arziki sosai.”
Ya kara da cewa, Bauchi tana da wadataccen filin noma, albarkatun kasa da muddin aka samu wani mai tunani na kwarai zai iya kyautata tattalin arzikin jihar da albarkatun da Allah ya wucewa wa jihar.
Ya daura da cewa, a dukkanin masu sha’awar tsayawa takara a jihar Bauchi babu wani da suke da yakini a kanshi illa Ambasada Tugga, yana mai karawa da cewa, nagartar dan takara shi ne abun nema.
Daga bisani ya jawo hankalin al’umma da su darje su zabi wanda ya dace domin kyautata jihar a kowani lokaci. Ya nemi masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da su yi la’akari da dacewar Tuggar wajen tsayar da shi a matsayin dan takara a yayin zaben 2023.
No comments