Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirye-shiryen kaddamar da takararsa na shugabancin kasa a zaben 202...
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirye-shiryen kaddamar da takararsa na shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Daily Nigerian ta rahoto.
Da ya ke magana yayin taron manema labarai a ranar Juma'a, Kwankwaso ya ce ya tuntubi mutane da dama kuma sun bashi goyon baya.
"Na tuntubi abokai na da yan Najeriya daga bangarori da dama kuma na samu goyon baya. Zan sanar da yan Najeriya takara ta mako mai zuwa," in ji shi.
News Digest ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya nuna gamsuwarsa bisa goyon bayan da NNPP ke samu duba da yadda mutane ke rajista a jam'iyyar.
Ya kara da cewa zaben 2023 za a fafata ne tsakanin wadanda ke son canji da wadanda ke son lamura su cigaba a yadda suke a yanzu.
No comments