Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

2023: Matar Tinubu Ta Kaurace Wa Shan Ruwan Da Osinbajo Ya Shirya Wa Sanatocin APC

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya amshi bakwancin Sanatocin APC don yin liyafar bude bakin Azumi a gidansa na Aguda da ke cikin fad...


Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya amshi bakwancin Sanatocin APC don yin liyafar bude bakin Azumi a gidansa na Aguda da ke cikin fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Sanatoci biyu daga cikin uku da suka fito daga jihar Legas Sanata Solomon Adeola Olamilekan da Tokunbo Abiru dukkaninsu sun halarci liyafar illa Sanatar da ke wakiltar mazabar Legas ta tsakiya matar jigon APC Ahmed Tinubu, Madam Oluremi Tinubu da ta kaurace wa liyafar.

Liyafar cin abincin da aka shirya tare da gayyatar zababbun sanatocin APC na da manufar jan ra’ayinsu da su dafa wa muradin Osinbajo na neman shugabancin Nijeriya a 2023.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan shine ya jagoranci Sanatocin a yayin ganawar.

Mataimakin shugaban kasa ya yi cikakken bayani wa sanatocin kan niyyar da ke da shi na neman shugaban kasa tare da bidar goyon bayansu don ganin ya samu cimma nasarar da ya sanya a gaba.

Wannan tattaunawar na daga cikin matakan da Osibanjo ke dauka na tuntuba da neman shawarorin masu ruwa da tsaki kan wannan niyyar tasa na neman kujerar shugaban kasa.

Da ya ke ganawar ya kasance a sirrance ne, bayan ganawar Ahmad Lawan ya yi wa ‘yan jarida karin haske kan abubuwan da suka wakana a ganawar.

Ya ce mataimakin shugaban kasan ya musu bayani kan ra’ayin da ke da shi na neman shugaban kasa tare da neman shawarorin da yake yi a kai.

Ya ce a matsayinsu na sanatoci a shirye suke su Bada gundumawar su domin cigaban kasar nan da ‘yan kasa tare da tabbayar da an gudanar da zabe mai cike da gaskiya kuma sahihi a fadin kasar nan.

No comments