LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa; a ranar litinin 11 ga watan Afrilun 2022, Dan Buran Zazzau, Hon. Sani Sha’aban Mahmud, ya bayyana kuduri...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa; a ranar litinin 11 ga watan Afrilun 2022, Dan Buran Zazzau, Hon. Sani Sha’aban Mahmud, ya bayyana kudurinsa na takarar kujerar gwamnan Jihar kaduna a karkashin Jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023 da ke tafe.
Taron Wanda ya gudana a babbab dakin taro na Arewa House da ke Kaduna, ya samu halartar manya-manyan ‘yan siyasa maza da mata, inda da suka yi dafifi wajen nuna goyon bayansu ga Hon. Sani Sha’aban.
Da yake jawabi a wurin taron, Hon. Sani Sha’aban, ya ce wannan shi ne karo na uku da yake takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna tun daga shekarar 2007 da ya fito a Jam’iyyar ANPP da kuma shekarar 2011 da ya fito a karkashin inuwar Jam’iyyar ACN, duk da zummar kawo ingantaccen shugabanci a Jihar kaduna.
A wannan karon ya ce, ya fito a karkashin inuwar Jam’iyyar APC ne domin ya ci gaba da ayyukan Alkhairi da gwamna Malam El-rufai yake yi da kuma magance matsalar tsaro da ta yi wa Jihar katutu, musamman a yankunan Birnin Gwari, Giwa da sauran sassan Kudancin Kaduna.
Sha’aban, ya kara da cewa muddin ya samu nasara zai yi kokarin ganin ya inganta rayuwar alumar Jihar kaduna ta bangarori daban daban.
A nasa jawabin a wurin taron, tsohon wakilin karamar hukumar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilai ta tarayya, Muhammad Sani Ibrahim Wakilin Jama’a, ya bayyana goyon bayansa ga takaran Hon. Sani Sha’aban, inda ya bukaci alumar Jihar Kaduna da su ba shi dama domin bada tasa gudunmawar wajen ciyar da Jihar Kaduna gaba, duba da irin tarin kudurorin da yake da su na ci gaba.
Kazalika, Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau, Alhaji Ibrahim Idris, ya bayyana irin halayya ta kirki da Hon. Sani Sha’aban yake da su, inda yace muddin aka zabe shi zai gudanar da ayyukan ci gaba da dama.
A nasa tsokacin Hon. Usman Bello Abubakar, ya bayyana irin manufofin Hon. Sani Sha’aban, kama daga inganta Ilimi da samar da tsaro da aikin yi da kuma walwalar Jama’a. Don haka ya bukaci alumar Kaduna da su mara masa baya domin kwankwadar romon demokradiyya.
Daraktan yada labarai na kungiyar, Sani Sha’aban Support Group, Ibrahim Auwal, ya bayyana irin shirin da suka yi musamman wajen wayar da kan Jama’a da sanar da mutane irin kudurori da tanadin alkairan da suke tattare da zaban Hon. Sani Sha’aban a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
No comments