Hukumomin Afirka da Kudu suka ce adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a birnin Durban da ke kusa da tashar jiragen r...
Hukumomin Afirka da Kudu suka ce adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a birnin Durban da ke kusa da tashar jiragen ruwa na kasar ya kai 306, bayan da shafe hanyoyi da tsaunuka, tare da lalata gidaje da gadoji.
Da farko babbar jami’ar kula da lafiya a yankin da aka samu iftila’in Nomangugu Simelane-Zulu ta tabbatar da adadin, inda take cewa ya zuwa daren Talata sun aje gawarwakin mutane 253 a asibitocin su guda biyu.
Jami’ar ta ce ya zuwa wannan lokaci suna cikin fargaba, domin dakin ajiye gawarwakin ya cika ya batse, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.
Shugaban kasa Cyril Ramaphosa wanda ya ziyarci yankunan da aka samu hadarin yace da sun saba ganin iftila’in na afkawa wasu kasashe irin su Mozambique da Zimbabwe, amma yau gashi suna gani a gida.
Rahotanni sun ce an kwashe shekaru 60 ba’a taba ganin irin ruwan saman da aka gani jiya ba, wanda ya rusa gidaje da gadoji da wanke hanyoyi da kada turaku da kuma tarwatsa kwantainoni a tashar jiragen ruwan kasar.
No comments