Shugaban majalisar dattawa Najeriya, Ahmad Lawan ya roki ‘yan Najeriya da su sake baiwa jam’iyyar APC mai mulki wata dama. Ya bayyana ha...
Shugaban
majalisar dattawa Najeriya, Ahmad Lawan ya roki ‘yan Najeriya da su sake baiwa
jam’iyyar APC mai mulki wata dama.
Ya
bayyana haka ne a wani taro da Sanata mai wakiltar Kwara ta tsakiya, Dokta
Ibrahim Yahaya Oloriegbe ya shirya a Ilori ranar Asabar.
Shugaban
majalisar dattijai ya kaddamar da ginin wata cibiya ta gyaran hali a asibitin
masu tabin hankali na tarayya da ke Budo-Egba a karamar hukumar Asa, sannan ya
kaddamar da cibiyar kula da lafiya ta Idi-Isin Community Heatlh Centre da ke
Unguwar Okolowo a Ilorin, wanda Oloriegbe ya gina.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, wanda lawan ya gada, na daga cikin wadanda suka wakilci mazabar Oloriegbe a Majalisar.
No comments