Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Akwai Rufin Asiri A Noman Albasa, Inji Alhaji Yunusa Fambeguwa

Daga Umar Idris Kaduna A cikin satin da ya gabata ne daya daga cikin 'ya'yan ƙungiyar masu noman albasa da sarrafa ta ha...


Daga Umar Idris Kaduna

A cikin satin da ya gabata ne daya daga cikin 'ya'yan ƙungiyar masu noman albasa da sarrafa ta har da sayarwa na garin Fambeguwa ta jihar Kaduna, Alhaji Yunusa Fambeguwa ya zanta da manema labarai yayin ziyara sada zumunci da ya kawowa 'ya'yan ƙungiyar na reshen karamar hukumar Zariya.

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Alhaji Yunusa ya fara ne da godewa Allah madaukakin Sarki da yasa shi cikin masu noman Albasa a fadin kasar Arewa baki daya.

Manomin ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu wani manomin Albasa a fadin kasarmu Nijeriya da bai san shi ba bisa ga rufin asiri da Allah ke bayarwa a fannin noman Albasa a halin yanzu. 

Alhaji Yunusa ya ce a halin yanzu ya kai shekaru 45 a duniya kuma noman albasa ya tasa a gaba don haka yasan dadin noman albasa ya san wahalarta. Ya ce yanzu haka yana noman albasa a kasar Kura ta jihar Kano yanayi a Gafai yanayi a Ciromawa.

Bisa haka ne ma ƙungiyoyi da dama suka sashi cikin tafiyarsu musamman kungiyar PCRC da ƙungiyar 'yan kasuwa yanzu haka muna tare da su don ci gaban jama'a a cewarsa. 

Alhaji Yunusa ya kara da cewa a lokutan baya shi manomin Tumatur ne da sauransu amma yanzu bisa ga yadda ya gano bakin zaren a noman Albasa tuni ya ajiye sauran ya koma noman albasa tsantsa.

Da yake bada shawara ga masu sha'awar fara noman albasa, ya fara ne da cewa wajibi ne a sami ilmin irin tukunna wato a gane irin da ake yinsa da Rani da irin da ake yafa shi cikin damina daga nan sai Ilmin wajen noma ta wato kwari ko tudu daga nan sai a nemi ilmin yafi da dashenta karshe ne sai a nemi ilmin adana ta wato ajiye ta inda ba za ta lalace ba.

Alhaji Yunusa ya yi kira ga  gwamnati da su duba kokari irin na manoma albasa a kasa baki daya don haka ne ya ce ya kamata duk lokacin da za a bayar da tallafin noma to a tuna da manoman albasa a kasa baki daya. 

Karshe ya yi kira ga 'ya'yan ƙungiyar masu noman albasa baki daya da su hada kai su zama tsintsiya madaurinki daya don cin gajiyar juna, ya ce yanzu haka suna tare da ƙungiyar ta ƙasa wajen kawo cigaban manoman albasa da masu sarrafa ta da masu sayarwa baki daya kuma ya yi fatan alheri ga shugaban na kasa baki daya Alhaji Isa Aliyu Binji Sokoto.

No comments