Akwai Yiwuwar A Yi Azumi 30 A Jamhuriyyar Kasar Nijar


Masana ilimin taurari a Nijar - kamar Najeriya da Saudiyya da Faransa - sun ce akwai yiwuwar a yi azumi 30 saboda babu tabbas ko za a ga watan Shawwal a yau Asabar.

Babban malamin Musulunci Sheikh Bourema Abdou ya ce hatta a garuruwan Zinder da kuma Diffa, inda rana ke riga faɗuwa, babu tabbas ko za a ga watan.

Tuni Saudiyya ta sanar cewa sai Litinin za ta yi bukukuwan Ƙaramar Sallah, inda za a yi azumi 30.

Post a Comment

0 Comments