Babban Limanin Masallacin Apo Legislative Quarters Mosque, Sheikh Nuru Khalid, wanda aka dakatar kan wa'azin da ya yi da ake yi wa kal...
Babban Limanin Masallacin Apo Legislative Quarters
Mosque, Sheikh Nuru Khalid, wanda aka dakatar kan wa'azin da ya yi da ake yi wa
kallon na 'sukar gwamnati' ya yi magana a karon farko, kamar yadda Jaridar The
Punch ta labarto.
Khalid, wanda aka fi sani da Digital Imam, a cikin
wani sako da ya wallafa cikin harshen larabci ya ce, "Allah ne mafi girma
da buwaya. Shi ya ke bada mulki kuma ya karba daga hannun duk wanda ya ga dama
lokacin da ya ga dama."
Wannan sakon ya yi kamanceceniya da sakon da ke
cikin wasikar da Sanusi Lamido II ya rubuta lokacin da aka tube shi a matsayin
sarkin Kano.
Babban malamin ya kuma bukaci yan Najeriya su cigaba
da yi wa kasarsu da shugabanni addu'a. Ya ce, "Ya Allah! mai girma da
buwaya, kai kake bada mulki ga wanda ka ke so, kuma ka kwace daga wanda ka ke
so, ka ke daukaka wanda ka ke so kuma ka kaskantar da wanda ka ga dama, dukkan
alheri na hannun ka, lallai kai ke da iko a kan komai." A ranar 1 ga waan
Afrilu ne kwamtin masallacin Apo Legislative Quarters ta dakatar da Khalid bisa
wa'azin da ya yi a ranar Juma'a.
A cikin wa'azin, Khalid ya caccaki gwamnati kan
gazawarta wurin samar da tsaro a kasar nan. Malamin ya fada wa masu zabe kada
su zabi duk wani dan siyasa da ba zai iya tabbatar musu da tsaron rayuka da
dukiyoyinsu ba.
No comments