Hukumar shirya gasar Firimiya ta Nijeriya, LMC, ta ci tarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars naira miliyan 9 bayan saɓa ƙa&...
Hukumar shirya gasar Firimiya ta Nijeriya, LMC, ta ci tarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars naira miliyan 9 bayan saɓa ƙa'idodi da dokokin shirya gasar.
Za a kwashewa Pillars É—in maki uku daga adadin makin da ta tara a kakar bana. Haka idan ta sake aikata laifi a nan gaba, za a sake kwashe mata maki uku.
Daga yanzu ƙungiyar za ta dinga buga wasannin ta na gida ne a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja.
An dakatar da filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata daga ɗaukar dukkanin wasannin gasar NPFL har sai abin da hali ya yi.
Kano Pillars za ta sauya/gyara motar Katsina Utd da magoya bayanta suka lalata.
No comments