Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Kashe Kusan Mutum Dubu 3 Da Sace Sama Da Dubu 1 A Cikin Wata Uku A Nijeriya

  Jana'izar wasu manoma da Boko Haram ta kashe a shekarar 2022 a jihar Borno.  Wani rahotan binciken da aka gudanar a Nijeriya yace muta...

 

Jana'izar wasu manoma da Boko Haram ta kashe a shekarar 2022 a jihar Borno. 

Wani rahotan binciken da aka gudanar a Nijeriya yace mutane 2,968 'yan bindiga suka kashe a Jihohin Neja da Kaduna da Zamfara a cikin watanni 3, yayin da aka yi garkuwa da wasu 1,484.

Binciken da kungiyar sanya ido akan harkokin tsaron Najeriya ta gudanar da ake kira ‘Nigeria Security Tracker’ yace mutanen da ake kashewa a yankin Arewa Maso Yammacin kasar ya zarce wanda akeyi a kowanne sashe.

Rahotan binciken da Jaridar Premium Times ta wallafa yace ‘Yankin Arewa ta tsakiya itace ta biyu wajen kashe kashen, inda tayi asarar mutane 984, sai kuma Arewa maso Gabas wadda tayi asarar mutane 488.

Yankin Kudu

A yankin kudu maso gabashin kasar inda ake fama da masu fafutukar kafa kasar Biafra, an hallaka mutane 181 a wadannan watanni, yayin da aka kashe mutane 127 a Kudu maso Yamma da 85 a Kudu maso Kudu.

Arewa maso Yamma

‘Yan bindigar da aka bayyana a matsayin ‘Yan ta’adda na ci gaba da kai munanan hare hare Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda suke hallaka mutane tun daga shekarar 2017.

Wadannan mahara sun kashe mazauna karkara da kwashe dukiyoyin su da kuma garkuwa da wasu daga cikin su domin karbar diyya, yayin da manoma da matafiya ma basu tsira ba daga hare haren wadannan mutane.

Arewa maso Gabas

Yayin da Yan bindigar ke hallaka jama’a a Arewa maso Yamma, mayakan boko haram na ci gaba da kai hare hare a yankin Arewa maso Gabas.


-Rahoton RFI Hausa

No comments