Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari a ga Mubarak Bala, haifaffen Kano wanda ya yi ridda, bayan da ya amsa laif...
Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari a ga Mubarak Bala, haifaffen Kano wanda ya yi ridda, bayan da ya amsa laifuffuka 18 da suka shafi tada zaune tsaye da kuma rashin zaman lafiya da ake yi masa.
Bala, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Ƴan Adam ta Nijeriya, an kama shi ne a gidansa da ke Kaduna a ranar 28 ga Afrilu, 2020 kuma aka taho da shi Kano, inda aka kai kararsa kotun a kan kalaman batanci ga addinin musulunci da kuma tunzuri.
A baya dai ya wallafa kalaman batanci ga Musulunci, Allah da kuma Annabi Muhammad (SAW) a shafin Facebook, lamarin da ya harzuka Musulmai.
An dai yi kamfen a sake shi ko kuma a yi masa shari’a, inda masu fafutuka ke cewa an raba shi da samun gana wa da matarsa da lauyansa.
Amma da ya bayyana a gaban mai shari’a Farouk Lawan na babbar kotun Kano ta 4 da ke Sakatariyar Audu Bako a yau Talata, Bala ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Da Alkali ya tambaye shi ko ya san sakamakon amsa laifinsa da ya yi, sai Bala ɗin ya kafe kan cewa ya aikata laifin kamar yadda ya faɗa da farko.
Lauyan Bala, James Ibor, a baya ya yi kokarin shawo kan wanda ya ke karewa ya sauya rokonsa, amma ya dage cewa yana da laifi kan tuhumar da ake masa.
Sai dai lauyan ya bayyana takaici da fargaba a matsayin dalilan da suka sa wanda yake karewa ya amsa laifinsa, inda ya ce wanda yake karewa ya shafe shekaru biyu a gidan yari.
Sai dai kuma shi Bala ɗin, wanda ya bayyana a gaban kotun ba tare da tada hankali ba, ya daga hannu ya shaida wa kotu cewa ya aikata laifin kamar yadda ake tuhumarsa.
A cikin rokonsa na neman a yi masa sassauci, Bala ya ce manufar rubutun da ya yi a shafukan sada zumunta ba shi ne ya haifar da tashin hankali ba. Don haka ya yi alkawarin ba zai sake maimaita irin wannan aika-aikar ba a nan gaba.
Da yake zartar da hukuncin, Mai shari’a Lawan ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari.
No comments