Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Yi Wa Malamin Jami’a Da Wani Tela Kisan Gilla Bayan Idar Da Sallar Asham A Jos

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa; wadansu ‘yan ta’adda sun kai wa wasu bayin Allah hari, ciki harda wani Malamin Jami’a, inda su...


LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa; wadansu ‘yan ta’adda sun kai wa wasu bayin Allah hari, ciki harda wani Malamin Jami’a, inda suka yi masu kisan gilla bayan idar da Sallar Asham a ranar Litinin 10, ga watan ramadana a birnin Jos na Jihar Filato.

‘Yan ta’addan sun kashe, Sani Mazadu, wanda malami ne a Jami’ar gwamnatin tarayya da me garin Gashua Jihar Yobe.

Maharan sun kuma kashe wani mutum mai suna, Safiyanu Sa’eed, ya kasance yana sana’ar dinki, mutanen biyu sun samu yabo da kyakkyawar shaida daga mutanen yankin.

Jihar Filato, Jiha ce ta yi kaurin suna wurin rikice-rikicen Addini da kabilanci da hare-haren ‘yan bindiga musanman a baya-bayan nan da suka addabi wasu kauyukan Jihar da dama.

No comments