Da safiyar yau Asabar 22 ga watan Ramadan ne da misalin ƙarfe 10:00am na safe daidai wakilin Jaridar MADOGARA ya yi ira da Ɗalib...
Da safiyar yau Asabar 22 ga watan Ramadan ne da misalin ƙarfe 10:00am na safe daidai wakilin Jaridar MADOGARA ya yi ira da Ɗalibin Madrasatu Amiril Mu'minin (A.S) dake Anguwar Jaba a ƙaramar Hukumar Sabon Garin Zariya ta jihar Kaduna. Ɗalibin mai suna Hassan Abdurra'uf, an tattauna da shi ne dangane da Azumin watan Ramadan na bana.
Ga taƙaitacciyar hirar da muka yi da shi kamar haka;
TAMBAYA: Mene ne Sunanka?
Amsa: Sunana Hassan Abdurra'uf.
TAMBAYA: Shekarunka nawa?
Amsa: Shekaru na bakwai (7).
TAMBAYA: Azumi nawa ka yi a wannan wata na Ramadan mai Albarka?
Amsa: Azumina Ashirin da biyu (22) daidai da naka idan na kai wannan.
TAMBAYA: Masha Allah. Masu karatunmu za su so su ji yadda ka iya yin azumi Ashirin da biyu?
Amsa: kawai na yi ne.
TAMBAYA: Azumin bai baka wahala?
Amsa: Yana bani wahala sosai.
TAMBAYA: Ƙarfe nawa kake shan ruwa?
Amsa: Ƙarfe bakwai da kwata 7:15pm.
TAMBAYA: Idan ka É—auki azumi a gida kake zama har sai an sha ruwa ko akwai inda kake zuwa?
Amsa: Ina zuwa kasuwa wajen babanmu, Idan aka tashi ya bani kuÉ—in shan ruwa. Sannan kuma ina zuwa makaranta.
TAMBAYA: Yanzu Azumi nawa kake so ka yi a wannan shekarar?
Amsa: Talatin ba biyu.
TAMBAYA: Ko mene ne dalilin da yasa kake son shan É—ayan?
Amsa: Haka nan kawai.
TAMBAYA: Me zai hana ka yi dukka ko dai kana son sha ne?
Amsa: A'a, zanyi to.
Mai karatun mu wannan ita ce taƙaitacciyar hirar da muka yi da Ɗalibi Hassan Abdurra'uf ɗan shekaru bakwai a duniya da Haihuwa, amma kunga yadda ya dage yana yin azumi ba fashi. Kana ganin wannan kasan tarbiyya ce da ya samu a gida dangane da Ibada.
A shari'a dai azumi bai zama wajibi akan shi ba sai ya kai shekarun takalifi, amma kunga yadda ya dage da azumi tun kafin ya kai waÉ—annan shekarun. Wannan tarbiyya ce.
Allah ta'ala ya ci gaba da inganta rayuwarsa. Ya biyawa Iyayenshi buƙatunsu na Alkhairi.
No comments