Hukumar zaben Najeriya tace duk da matsalolin tsaron da ake fuskanta a wasu sassan kasar, babu abin da zai hana gudanar da zaben shekara m...
Hukumar zaben Najeriya tace duk da matsalolin tsaron da ake fuskanta a wasu sassan kasar, babu abin da zai hana gudanar da zaben shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da haka lokacin da yake gabatar da tsare tsaren da suka shirya zai kankama daga shekaran nan ta 2022 zuwa shekarar 2026.
Yakubu yace tabbas akwai kalubale sosai dake gaban Hukumar tasa, musamman matsalolin tsaro wadanda ke yiwa jami’an su barazana, amma duk da haka suna tattauna da jami’an tsaro domin tsara yadda za’a gudanar da zaben ba tare da matsala ba.
Shugaban Hukumar zaben ya roki Yan Najeriya da su hada kai da hukumar ta su wajen ganin an samu nasarar zaben, yayin da ya bukaci Jam’iyyun siyasa da su mutunta jadawalin tsarin zaben kamar yadda aka gabatar da shi.
Farfesa Yakubu yace akalla ma’aikata kusan miliyan guda ake saran su yiwa Hukumar aiki a mazabu dubu 176,846 dake kananan hukumomi 774 dake Najeriyar.
No comments