Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Babu Shugabanci A Nijeriya –Farfesa Jega

  Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa , INEC , Farfesa Attahiru Jega, a ranar Asabar ya ce gwamnati a dukkan matakai sun y...

 


Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega, a ranar Asabar ya ce gwamnati a dukkan matakai sun yi watsi da harkokin mulki.

Ya yi wannan tsokaci ne a taron jam’iyyar PRP na kasa da aka gudanar a Abuja.

“Gwamnatoci a matakin jiha, kananan hukumomi da Tarayya sun dade da yin watsi da harkokin mulki,” inji shi. “Kuma babu wata kasa da za ta ci gaba ba tare da shugabanci na gari ba, ba tare da nagartattun mutane da za su yi jagoranci da shugabanci nagari ba.

“Don haka ina rokon mu da mu koma mu gane cewa aikin da ke gabanmu yana da yawa; yana iya ma zama yana da wahala, amma yin hakan ba zai gagara ba.”

Farfesa Jega dan jam’iyyar PRP ne.

Jam’iyyar na fatan kara yawan membobinta zuwa 30,000 a kowace jihohi 36 na Tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

A taron na ranar Asabar, jam'iyyar ta rantsar da sabbin shugabannin zartaswa na kasa.

Jam’iyyar PRP na alfahari da kanta a matsayin jam’iyyar siyasa mafi dadewa a Nijeriya, tun da farko an yi mata rajista a shekarar 1978.

A cewar shugaban jam’iyyar na kasa, Falalu Bello, jam’iyyar PRP na tattaunawa da sauran kungiyoyin siyasa domin hadewa, amma ba ta shirya sauya suna ko tambarin ta ba.


No comments