Wata kotun soji a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai-da-rai, kan kisan gillar da aka yi wa...
Wata kotun soji a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai-da-rai, kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Shugaban juyin juya hali na kasar Thomas Sankara a shekarar 1987.
Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga
Hyacinthe Kafando, jami'in da ake zargi da jagorantar rundunar da aka kai harin
shekaru 37 da suka gabata, da kuma Janar Gilbert Diendere, kwamandan sojoji a
lokacin kisan.
Blaise Compaore mai shekara 71 a duniya, wanda ke
gudun hijira a kasar Ivory Coast bayan da aka hambarar da shi sakamakon
zanga-zangar da jama'a suka yi a shekarar 2014, da kuma Kafando, wanda ke gudun
hijira tun 2016, an yi musu shari'ar ne a bayan idonsu.
No comments