Buhari Ya Gana Da Sabon Shugaban Jam'iyyar APC A Fadar Aso Rock

 


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu a Fadar Aso Rock da ke Abuja.

Tsohon shugaban riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya raka sabon shugaban.

Wannan ne karo na farko da Sanata Abdullahi Adamu ke kai ma Shugaba Buhari ziyara tun bayan da aka kammala babban taron jam'iyyar a Abuja.

Ganawar na da nasaba da shirye-shiryen da jam'iyyar ke yi na zabukan fitar da gwani domin tunkarar babban zabe na kasar da za a yi a shekara 2023.

Post a Comment

0 Comments