Rfi Hausa ta labarto cewa; Babban Limamin mabiya darikar Katolika dake Sokoto, Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewar shugaban kasa M...
Rfi Hausa ta labarto cewa; Babban Limamin mabiya
darikar Katolika dake Sokoto, Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewar
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala lalata duk wani bangare na rayuwar
jama’ar kasar a karkashin gwamnatinsa tare da bai wa cin hanci da rashawa damar
habaka.
Yayin da yake gabatar da sakon bikin Easter a
mujami’ar sa, Kukah ya ce duk wani bangaren rayuwar jama’ar Najeriya ya lalace,
yayin da kasar ta zama sashen gobe da nisa na asibiti dauke da tarin marasa
lafiya.
Limamin ya ce zukatan ‘Yan Nijeriya tare da iyalansu
da gidajensu da Mujami’u da Masallatai da kayan more rayuwa duk sun ruguje a
karkashin gwamnatin Buhari.
Kukah ya ce harkokin ilimin kasar ya ruguje tare da
rayuwa da makomar ’yaran kasar kamar yadda bangaren siyasa da tattalin arziki
da makamashi da al’ummomi da hanyoyin mota da na jiragen kasa suka ruge inda
babu abin da ke rayuwa yadda ake bukata da ya wuce cin hanci da rashawa.
Limamin ya ce yau ‘Yan Nijeriya basa iya gane kasar
su saboda yadda ta fita daga cikin hayyacin ta sakamakon matsalolin da suka
mamaye ta a karkashin gwamnatin Buhari.
Kukah yace lura da irin wadannan dimbin matsalolin
da suka addabi Najeriya wasu ‘Yan kasar na tambayar ko masu rike da madafun
ikon a basa ji ko gani ko dandanar irin yanayin da jama’ar kasar suka samu kan
su ne ko kuma suna nuna halin ko-in-kula ne domin babu abinda ya dame su.
Limamin y ace babban kalubalen dake gaban jam’ar
Najeriya ayau itace yadda za’a fara daukar matakin sake dawo da kimar kasar da
fatar mutane zasu rayu har zuwa lokacin zaben shekara mai zuwa da kuma sanya
ido akan abinda zai biyo baya domin fuskantar matsalolin da suka addabi kasar
ta hanyar gina halayen jama’a da kuma son kasa.
Kukah ya bukaci shugabannin addinai da su tashi
tsaye cikin gaggawa domin ceto Najeriya daga halin da ta samu kanta, musamman
ganin yadda yanzu ake samun miliyoyin mutane a cikin kasar da duniya baki daya
dake barin addinin Krista da Musulunci domin zama marasa addinai.
No comments