Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Chelsea Za Ta Hadu Da Liverpool A Wasan Karshe Na Kofin FA

  Chelsea za ta yi haduwa karo na biyu a Wembley da Liverpool a kakar wasa ta bana bayan da ta doke Crystal Palace da ta nuna juriya da ci 2...

 


Chelsea za ta yi haduwa karo na biyu a Wembley da Liverpool a kakar wasa ta bana bayan da ta doke Crystal Palace da ta nuna juriya da ci 2 – 0 ta kuma haye wasan karshe na cin kofin FA.

Liverpool ta lashe gasar kofin Carabao a bugun fenariti a watan Fabrairu amma wata kila Chelsea ta samu damar ramawa a haduwar da zasu yi a wasan karsha na kofin FA.

Karo na uku kenan a jere Chelsea ke kaiwa wasan karshe na cin kofin FA, sai dai tana fatan tarihi a sauya a wannan karo, bayan ta sha kashi a haduwar biyu da suka gabata a hannun Arsenal da Leicester City.

Kociyan kungiyar Thomas Tuchel na da gagarumin tarihi wajen kaiwa ga wasan karshe na gida da na Turai tun bayan zuwansa Chelsea, yayin da ta kasance babbar abokiyar hamayyar Liverpool, wanda ke neman kofin karo na hudu mai tarihi.

No comments