Gwamnan Jihar Binuwe Samuel Ortom ya bayyana dalilin da zai hana baiwa ‘yan kabilar Idoma damar zama Gwamna a Jihar a zaben shekara mai zu...
Gwamnan Jihar Binuwe Samuel Ortom ya bayyana dalilin
da zai hana baiwa ‘yan kabilar Idoma damar zama Gwamna a Jihar a zaben shekara
mai zuwa, sabin alkawarin da yayi a shekarun baya cewar a shirye yake ya ga sun
karbi mulki a karon farko.
Daga cikin dalilan da Ortom ya gabatar a matsayin
abinda zai hana Idoma zama gwamna a Benue harda da rashin hadin kai a tsakanin
kananan hukumomi guda 9 dake ke Yankin su da kuma rashin amincewa a tsakanin
manyan jam’iyyun jihar na daukar matsayin baiwa yankin takarar gwamna a shekara
mai zuwa.
Gwamnan ya shaidawa Jaridar Premium Times cewar idan
yanzu jam’iyyar sa ta PDP ta tsaida ‘dan takara daga Yankin Idoma, yayin da APC
ta tsayar daga Yankin Tibi, APC zata samu nasara domin Yankin Tibi ke da kahsi
biyu bisa 3 na al’ummar Jihar, saboda haka ya dace jam’iyyun gaba daya su yanke
hukuncin tsayar da takara daga yankin kafin a cimma nasarar samun gwamna daga
wancan bangaren.
Tun da aka dawo da mulkin dimokiradiya a shekarar
1999 Yan kabilar Tibi ne ke zama Gwamnan Jihar Benue, yayin da Yan kabilar
Idoma ke zama mataimaka.
Duk wani yunkuri na ganin kujerar gwamnan jihar ya
koma bangaren Idoma yaci tura saboda yadda jama’ar Tibi suka mamaye kasha biyu
bisa 3 na al’ummar jihar baki daya.
No comments