Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Dalilan Da Ya Sa Na Yi Murabus Daga Majalisar Dattawa -Shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu

Shugaban jam’iyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa na É—an majalisar dattawa, mai wakiltar Nasarawa ta Arew...


Shugaban jam’iyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa na É—an majalisar dattawa, mai wakiltar Nasarawa ta Arewa.

Sanata Adamu ya aikewa majalisar wasikar sauka daga mukaminsa ne bayan zabarsa da aka yi a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na Najeriya a Ranar 26 ga watan Maris.

Ya ce matakin da ya É—auka na barin majalisar ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilun da muke ciki.

Shugaban majalisar Dattawa Dakta Ahmad Ibrahim Lawal shi ne ya karanto wasikar da Shugaban jam’iyar APC na Æ™asa ya aike wa majalisar  a zaman ta na yau Talata.

A cikin wasikar tasa ya yabawa shugabancin majalisar karkashin jagorancin Sanata Ahmad Lawal.

“Ya zame min dole na yaba da salon jagorancinka mai cike da kwarjini da adalci ta yadda kake bawa ko wanne Sanata damarsa ba tare da nuna bambancin Jam’iyya ba.” Inji Sanata Adamu.

Kafin yayi murabus daga kujerar Dan majalisar Dattawan, Abdullahi Adamu ya rike mukamin gwamnan jihar ta Nasarawa har wa’adi biyu daga shekarar 1999 zuwa 2007 sannan Kuma yaci gaba da zama a majalisar Dattawa har karo uku.

No comments