Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Takarar Jam’iyyar PDP Na Maslaha: Shugabannin Arewa Sun Zabi Saraki Da Bala Mohammed

Daga Muhammad Farouk Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar PDP, shugabannin Arewa a ranar Juma'a 28 ga...


Daga Muhammad Farouk


Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar PDP, shugabannin Arewa a ranar Juma'a 28 ga watan Mayu, sun zabi tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a matsayin 'yan takararsu. 

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Ango Abdullahi, shugabannin Arewa sun ce an kai ga zaben Saraki da Bala Mohammed ne bisa wasu sharudda da aka amince da su wajen tantance ‘yan takarar hudu da suka mika kansu ga tantancewar. 

Sanarwar ta kara da cewa: “A bisa manufar wannan tantancewar, an yanke shawarar cewa Gwamna Bala Mohammad daga yankin Arewa maso Gabas da kuma tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki daga yankin Arewa ta tsakiya, za a gabatar da su a matsayin ‘yan takarar maslaha na Arewa a yanzu.

“An yanke shawarar cewa a gabatar da wani jigo daga Arewa ta Tsakiya da kuma daya daga Arewa maso Gabas a matsayin ‘yan takarar Shugabanci daga Arewa.

"Su biyun kuma za a bukaci a sake tantance su ta yadda a karshe za a gabatar da daya daga cikinsu a matsayin dan takarar da aka amincewa, daga cikin hudun da suka gabatar da kansu daga Arewa.

Idan dai ba a manta ba, wasu jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa guda hudu a jam’iyyar PDP, sun gana, inda suka yanke shawarar takaita yawan ‘yan takarar da suka fito daga Arewacin Nijeriya, ta hanyar kulla yarjejeniya a tsakaninsu. 'Yan takarar da suka gabatar da kansu don amincewa su ne; Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Gwamna Bala Mohammed, Dr Bukola Saraki da Mohammed Hayatu-Deen. 

"Haƙiƙa wannan wani babban abin a yaba ne da kuma sadaukarwa mai girma ga soyayyar ƙasa da yankin arewa musamman a ɓangaren masu neman su huɗun. Sakamakon haka, dukkannin masu neman takarar su hudu sun ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, inda suka ba shi wa’adin jagorantar tafiyar domin cimma matsayar tsayar da dan takarar maslahar, kuma sun amince su bi sakamakon hukuncin.

“Tsohon shugaban kasan ya karfafa masu neman da su samu maslaha a tsakaninsu sannan su fito da dan takara daya, wanda bayan wasu kwanaki suka kai masa rahoto suka kuma bukaci ya zabo daya daga cikin hudun.

No comments