Wadansu fustattun ‘yan Nijeriya sun yi dafifi a gaban ofishin tsoshon shugaban kasar Nijeriya, Goodluck Ebele Jonathan, inda suka nemi da ...
Wadansu fustattun ‘yan
Nijeriya sun yi dafifi a gaban ofishin tsoshon shugaban kasar Nijeriya,
Goodluck Ebele Jonathan, inda suka nemi da ya sake tsayawa takarar shugaban kasa.
Hakan ya faru ne a yayin da Nijeriya ke kara kusanto da babban zaben 2023, a
ranar Juma'a masu zanga-zangar sun mamaye ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck
Jonathan a Abuja, suna kira gare shi da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa
a 2023.
Jama'ar sun kunshi maza
da mata da matasa, inda suka mamaye ofishin dauke da alluna da takardu na neman
tsohon shugaban kasar ya shiga takarar shugaban kasa, kamar yadda jaridar Vanguard
ta ruwaito.
Wasu daga cikin
fastocin da ke dauke da hotunan Jonathan an rubuta:
"GoodLuck
Jonathan, dole ne ka tsaya takara"
"Muna bukatar ka
daidata Nijeriya." Masoyan na Jonathan sun yi imanin cewa tsohon shugaban
kasar yana da tsarin da zai dawo da martabar Nijeriya tare da bai wa duk ‘yan Nijeriya
jin dadin da suke bukata.
Jaridar Daily Trust ta
nuna hotunan lokacin da jama'ar ke mamaye da ofishin na Jonathan. Mai magana da
yawun tawagar 'yan zanga-zangar, Mayor Samuel ya ce “Wadanda suka ce za su iya
a shekarar 2015 ne suka yaudare mu da wanke kwakwalen. Yanzu mun san cewa a
karkashin Jonathan mafi karancin albashi na iya sayen buhunan shinkafa daya ko
biyu. Me muke da shi a yau? Muna rokon Shugaba Jonathan ya gafarta mana, mun
gane kura-kuranmu, muna son ya dawo ya kammala abin da ya fara."
Magoya bayan GEJ a yayin zanga-zangar a Abuja.
No comments