Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis ya yi kira da a kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar Ukraine. Yayin gabat...
Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis ya yi kira da a kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar Ukraine.
Yayin gabatar da gabatar da sakon Easter da ke zuwa cikin rikicin Ukraine a dandalin Saint Peter da ke fadar Vatican, Ya ce akwai bukatar shugabannin kasashe su ji koken mutane na neman zaman lafiya.
Francis ya ce rikicin ya shafi ‘yan kasar Ukraine da dama inda miliyoyi suka zama ‘yan gudun hijira.
Har wayau, Fafaroma Francis ya kuma yi kira da a bai wa kowa damar shiga wuraren ibada masu tsarki a birnin Kudus.
Wannan dai na zuwa ne yayin da jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da raunatawa da kashe masallata Falasdinawa a masallacin Kudus.
No comments