Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidauniyar Asattahir Ta Ƙaddamar Da Fara Bincike Akan Musabbabin Tashin Gobara Da Kuma Hanyoyin Dakile Ibtila’in A Jihar Sokoto

A ranar 21 ga Afrilun shekara ta 2022 ne Gidauniyar ASATTAHIR (AIF) ta kaddamar da wani bincike mai taken “Shiri Domin Tunkarar ...


A ranar 21 ga Afrilun shekara ta 2022 ne Gidauniyar ASATTAHIR (AIF) ta kaddamar da wani bincike mai taken “Shiri Domin Tunkarar Ibtila’in Gobara da kuma Magance Matsalarta a Jahar Sokoto' a kokarin gano abubuwan da ke haddasa barkewar gobara, yawaitar ta, tasirinta da kuma shirye-shiryen al’umma na mayar da martani idan irin wannan bala'i ya faru.

A jawabinsa na bude taron, wanda ya assasa kuma shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar ASATTAHIR Aliyu Sidi Attahiru ya yi maraba da dukkan mahalarta taron kaddamar da horaswar ta masu kididdigar a ofishin gidauniyar da ke Sokoto, ya mika godiya ta musamman ga tawagar masu bincike na gidauniyar karkashin jagorancin shugaban tsare-tsare da bincike Rufus Yagkong bisa jajircewa da nuna hangen nesa akan zakulo musabbabai na ibtila’in gobarar da ta dade tana addabar jihar ba, har ma da shawarwarin yadda za a dakile aukuwar gobarar a nan gaba. 
Haka ma, shugaban gidauniyar ya bayyana cewa, a wani bangare na ka’idojin bincike, an nemi amincewa daga hukumomin da abin ya shafa musamman kananan hukumomi uku na Sakkwato ta Arewa, Sakkwato ta Kudu da Wammako inda za a gudanar da binciken.

Taron, ya samu halartar Barista Rashida Mohammad mashawarciyar gidauniyar kan harkokin shari'a, Comrade Hussaini Mohammed Aliyu, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Sokoto kan harkokin kare hakkin bil'adama, Dr. Garba Ibrahim daga Jami'ar Usmanu Danfodio da ke jihar Sokoto da kuma Farfesa Yahaya Tanko Baba, Sakataren gidauniyar, ma’aikatan AIF, masu kididdiga da masu sa kai.
Da ta ke tsokaci kan aikin, Barr. Rashida Mohammed ta yabawa shirin gidauniyar na fara wannan bincike. Ta kuma umarci masu kididdigar da su nuna gaskiya da sanin makamar aiki yayin tattara bayanai.

Shima a nashi jawabin, Dokta Garba Ibrahim ya baiwa ma su kididdigar shawarar su kasance masu gaskiya, jajircewa da mutuntawa yayin tattara bayanai. Ya yabawa gidauniyar bisa fitowa da shiraruwa daban-daban da kuma kasancewar ɗan adam a zuciyar gidauniyar a cikin dukkan ayyukanta.

Farfesa Yahaya Tanko Baba a cikin jawabinsa na rufewa, ya yi tsokaci ne ta hanyar jawo hankalin masu kididdigar kan ladubban bincike da matakan tantance bayanai kafin a amince da su a matsayin abin dogaro. Ya yi nuni da cewa gidauniyar ta dauki ingancin bayanai da muhimmanci saboda sakamakon bincike da shawarwarin da aka fitar za su yi tasiri kai tsaye ga rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.


A wannan taron dai, an horar da masu ƙididdigar sosai akan ɗa'a, hanyoyin, fasaha, wuraren bincike, da girman samfurin da ake sa ran za a samar da bayanai ta hanyar amfani da fasahar zamani. 

A karshen taron horaswar, shugaban gidauniyar ya kaddamar Aliyu Sidi Attahiru, ya kaddamar da kwamitin da aka dorawa alhakin wannan aikin.

No comments