Daga Idris Umar Kaduna Gwamnan Jihar Zamfara H.E. Bello Matawallen Maradun ya kaddamar da rabon motocin sintiri sama da dari bi...
Daga Idris Umar Kaduna
Gwamnan Jihar Zamfara H.E. Bello Matawallen Maradun ya kaddamar da rabon motocin sintiri sama da dari biyu 200 ga jami'an tsaron kasa da ke jihar Zamfara domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al'umar jihar Zamfara baki daya.
Haka zalika, Gwamnan ya biyo da raba motoci masu alfarma ga Sarakuna domin shawo kan matsalar tsaro ta hanyar dawo da Martabar Sarakunan a wajen al'ummar da suke shugabanta.
Tabbas ga wanda ya san hali irin na Mai Girma Gwamnan jihar Zamfara ya san cewa wannan kokarin ba bakon abu bane a gare shi.
Haka zalika duk wanda ya san Matawallen Muradun ya san shi da kishin jama'arsa musamman yadda jiharsa ta fada cikin mawuyacin hali. Bisa wannan dalilai ne yasa Mai Girma Gwamnan jihar ta Zamfara ya yi abin da wani Gwamna bai taba yin sa ba a jihohin Arewacin wannan kasa tamu Nijeriya.
Wannan ya nuna cewa tabbas maganar tsaro na cikin zuciyarsa ba kamar yadda wasu ke hange ba. Bai wa jami'an tsaro matoci don tabbatar da zaman lafiya abu ne mai kyau da tasiri a harkar zaman lafiya a irin halin da ake ciki a yanzu.
Bincike ya tabbatar da cewa, sanya Sarakuna a gefe wajen maganar samar da tsaro kuskure ne babba domin Sarakuna na da gayan muhimmanci a bangaren samar da tsaro. Don haka ne yasa dole a jinjinawa Gwamnan jihar Zamfara akan wannan namijin kokari da ya yi tare da kira ga sauran Gwamnoni da su yi koyi da halin Gwamnan na Zamfara wato Dakta Bello Matawallen Muradun.
Tuni al'umma suke jinjina ga Matawalle bisa ga wannan kokari irin nasa. Daga cikin abin da yasa suke nuna yabo da jinjina ga Gwamnan Matawalle shi ne; yayin da wasu gwamnonin ke tunani akan wasu abu na kashin kai to shi Matawallen Muradun tunaninsa na wajen al'ummarsa ne.
Yayin da wasu suka kasa hango muhimmancin Sarakuna Matawalle tuni ya hango tare da janyo su a jika tare da ba su manyan motoci domin taimaka masa wajen dawo da zaman lafiya a jiharsa baki daya.
Matsalar rashin kayan aiki ga jami'an tsaro na daga cikin abubuwan dake kawo tsaiko a wajen gudanar da aikin kare rayuka da dukiyoyin al'umar jihar Zamfara cikin birane da kauyaku.
Hakan yasa al'ummar jihar Zamfara da kasa baki daya ke yabo da jinjina ga Matawalle Muradun na bai wa jami'an tsaro motocin gudanar da aiki wannan lamari abin farin ciki ne matuka.
Tuni al'ummar wasu jihohi suka fara yin kira ga Gwamnoninsu da su yi koyi da Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Dakta Bello Matawallen Maradun.
A wani bangaren bincike ya nuna cewa jami'an tsaron jihar ta Zamfara tuni suka mike tsaye don sharewa Gwamnan jihar hawaye ta hanyar daukar alƙawarin gudanar da aikin tukuru a fadin jihar ta Zamfara baki daya.
Haka zakila a bangaren Sarakuna kuwa tuni suke yin fatan alheri ga Gwamnatin jihar ta Zamfara tare da jinjina ga Gwamnan jihar Zamfara bisa wannan namijin kokari da ya yi.
Jihar Zamfara jiha ce da take fama da matsalar tsaro mafi girma a cikin jihohin Arewa da kasa baki daya.
Haka zalika jiha ce da take matukar bukatar taimako a bangaren tsaro bisa yadda rahotanni suka nuna a baya da kuma yanzu.
Bisa haka ne ya sa bai wa jami'an tsaro da Sarakuna motoci masu alfarama ya burge al'ummar Nijeriya da ta kai suke yabo da jinjina a halin yanzu.
No comments