Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Nijeriya Ta Doɗe Layukan Waɗanda Ba Su Yi Rajistarsu Ba

  Gwamnatin Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da ke cikin kasar su hana masu amfanin da layukan tarho yin waya daga layukansu ida...

 


Gwamnatin Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da ke cikin kasar su hana masu amfanin da layukan tarho yin waya daga layukansu idan har ba su yi rajistarsu ba kuma ba su hada su da lambar zama dan kasa ba (NIN) daga yau Litinin 4 ga watan Afrilun 2022.

Hukumar da ke kula da batutuwan sadarwa a Najeriya NCC tare da hukumar da ke kula da kuma yin rajistar 'yan Najeriya (NIMC) ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa ta hadin gwuiwa da suka fitar.

Wannan matakin na nufin wadanda aka rufe layukansu saboda rashin hada su da lambar dan kasa ba za su iya kiran kowa ba, sai dai za a iya kiransu.

Ministan sadarwa na kasar Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kawo yanzu, ta mika lambobin waya miliyan 125 domin a hada su lambar dan kasa, kuma hukumar NIMC ta yi rajistar lambobin dan kasa miliyan 78 kawo yanzu.

Sanarwar ta ce "Muna ba dukkan wadanda aka dode layukansu daga yin waya, da su tafi cibiyoyin da ake yin rajista domin hada lambobin nasu da lambar dan kasa domin kamfanonin sadarwa su iya bude musu layukan nasu.

No comments