Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa’adu Abubakar Na III Har ya zuwa misalin karfe 7:40 na daren yau Juma’a babu labarin ganin jaririn wata ...
![]() |
Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa’adu Abubakar Na III |
Har
ya zuwa misalin karfe 7:40 na daren yau Juma’a babu labarin ganin jaririn wata
Ramadan a fadin Nijeriya.
Kwamitin
dake lura da duban wata na Nijeriya a karkashin fadar Mai Martaba Sarkin
Musulmi, Sultan Alhaji Sa’adu Abubakar Na III, wato ‘National Moon Sighting
Committee - NMSC of NSCIA’ ya wallafa a shafinsa na Facebook da misalin karfe
7:20 na daren yau cewa; har ya zuwa lokacin bai samu labarin ganin wata ba daga
garuruwan Bauchi, Gombe, Azare, Misau, Numan, Lagos, Kaduna, Abuja, Bajoga,
Nafada, da Maiduguri da sauran su.
Inda
suka nemi jin ta bakin masu bibiyarsu dake sauran garuruwa akan cewa ko suna da
labarin ganin watan?
Jaridar MADOGARA ta labarto cewa al’ummar Musulmin Nijeriya na ci
gaba da sauraren Kwamitin duban watan na Sarkin Musulmi domin fara azumin
Ramadana a gobe Asabar ko jinkirtawa zuwa Lahadi idan ba a samu labarin ganin
watan ba.
A SAUDIYYAH AN GA JARIRIN WATAN
RAMADAN
Hukumar
da ke kula da Masallatan Haramai ta bayyana cewa an ga jaririn watan Ramadan a
wasu sassan kasar Saudiyya, inda ta bayyana gobe Asabar a matsayin daya ga watan
Ramadan a kafatanin kasar.
Rahoton
ya ce an samu rahoton ganin watan a wurare daban-daban a fadin kasar.
No comments