Harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna: Shugaban Bankin Noma Ya Samu 'Yancinsa


Manajan-Darakta na Bankin Noma, Alwan Ali Hassan, ya shaƙi iskar ƴanci da ga hannun ƴan ta'addan da su ka tashi bam a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

A yayin harin ne kuma yan ta'addan su ka yi awon-gaba da wasu fasinjoji, ciki har da shi Hassan ɗin.

Wani ɗan uwan Manajan-Darakta ɗin ne ya shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa an sako shi a yau Laraba.

Ya kuma ce an biya kuɗin fansa masu yawa, amma bai fadi takameme ko nawa a ka biya ba.

Post a Comment

0 Comments