Gwamnatin tarayya ta dora alhakin harin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna na kwanakin bayan nan akan hadin gwiwar da ke tsakanin kungiyar Bok...
Gwamnatin tarayya ta dora alhakin harin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna na kwanakin bayan nan akan hadin gwiwar da ke tsakanin kungiyar Boko Haram da ‘yan bindiga.
Ministan yada labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako mako wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa a ranar Laraba.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnati na namijin kokari kan shawo gaban lamarin.
No comments