Hatsarin Kwale-kwale Ya Hallaka Mutum 26 A Sakkwato

 


Akalla mutane 26 suka mutu a Jihar Sakkwato sakamakon hadarin kwale kwale a kogin Shagari da ke Jihar.

Wani jami’in Mulki a Yankin Aliyu Dantani wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce daga cikin wadanda suka mutu akwai mata 21 da yara kanana guda 5, kuma tuni aka ciro gawarwakin su.

Dantani ya ce basu iya tantance yawan mutanen dake cikin kwale kwalen lokacin da aka samu hadarin ba, ko kuma dalilin da ya haifar da hadarin.

A watan jiya mutane 13 suka nitse a ruwa lokacin da suke tserewa hare haren Yan ta’adda a Jihar Neja.

Post a Comment

0 Comments