Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Hazikin Matashi Saddiq Musa Kaita Ya Zama Sabon Sardaunan Katsina

Daga Wakilinmu Mai Martaba Sarkin Katsina Dr Abdulmuninu Kabir Usman ya tabbatar wa Saddiq Musa Kaita da sarautar Sardaunan Kats...


Daga Wakilinmu

Mai Martaba Sarkin Katsina Dr Abdulmuninu Kabir Usman ya tabbatar wa Saddiq Musa Kaita da sarautar Sardaunan Katsina.

Sarkin Katsina ya tabbatar masa da sarautar ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannunsa a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.

"Na amince da ba ka Sarautar Sardaunan Katsina kamar yadda ka nema," kamar yadda Sarkin Katsina ya bayyana a cikin takardar.

Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar bikin naɗin nasa.

Saddik jika ne ta bangaren uba ga sarkin Fadan Katsina Isma’ila Damale wanda shi kuma ɗa ne ga Wazirin Katsina na farko Haruna Kaita.

Haka kuma ta bangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.

No comments