Fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin ɗan adam, Femi Falana, SAN ya yi kira ga Gwamnatin Taraiya da ta kuma yafe wa ƙananan ...
Fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin ɗan adam, Femi Falana, SAN ya yi kira ga Gwamnatin Taraiya da ta kuma yafe wa ƙananan ɓarayi da su ke gidajen yari bayan ta yafe wa wasu manyan ƙasar nan.
Falana ya yi kiran ne jiya Juma'a a Ikeja, Jihar Legas yayin maƙala da ƙaddamar da littafi da a ka gabatar domin tunawa da tsohon Kakakin ƙungiyar Afenifere, Yinka Odumakin.
A cewar Falana, da an yi yafiyar bai-ɗaya ba tare da son kai da zaɓen wasu sanannu a ƙasa ba, da sai a ga cewa yafiyar an yi ta ne bisa adalci da daidaito.
Kanfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Majilisar Ƙoli ta Ƙasa ce ta yafewa wasu masu laifi 159 a ƙasar nan.
Daga cikin waɗanda a ka yafe wa ɗin sun haɗa da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye da a ka ɗaure shi bisa laifin wawure Naira biliyan 1.6, sai kuma tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame da a ka ɗaure shi bisa almundahanar Naira biliyan 1.6.
Falana ya shawarci gwamnatin da kasa ta riƙa nuna bambanci a kan ƴan ƙasa cewa dole sai wanda ya ke cikin abin masu mulki ne zai rika samun dama.
No comments