Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jirgin Kasan Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Kano Ya Yi Hadari A Kaduna

  Wani jirgin kasa da ya taso daga Legas zuwa Kano ya yi hadari a yankin Farin Ruwa da ke garin Jaji a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna...

 


Wani jirgin kasa da ya taso daga Legas zuwa Kano ya yi hadari a yankin Farin Ruwa da ke garin Jaji a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar Kula da Jiragen Kasa shiyyar Arewa, Alhaji Bala Kawu ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da wakilinmu a daren ranar Alhamis.

A cewarsa, nan take direban jirgin ya riga mu gidan gaskiya bayan aukuwar hadarin.

Bala Kawu ya kuma bayyana cewa jirgin ya dauko lemon kwalba ne daga Legas a kan hanyarsa ta zuwa Kano kafin faruwar hadarin, wanda lalata layin dogon da wasu bata gari suka yi ne sanadi.

Kazalika, ya ce tuni aka dauki matakan gaggawa don gyara tare da suturta gawar direban.

No comments