Gidan Rediyon Faransa ya labarto cewa rahotanni daga Jihar Neja sun ce, yara kanana da shekarunsu suka kama daga 5 zuwa 12 sun rasa rayukans...
Gidan Rediyon Faransa ya labarto cewa rahotanni daga
Jihar Neja sun ce, yara kanana da shekarunsu suka kama daga 5 zuwa 12 sun rasa
rayukansu, sakamakon harin da wani jirgin yakin Nijeriya ya kai a yankin
Kuregba da ke karamar hukumar Shiroro.
Wasu mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust
da ake wallafa ta a Najeriya cewa, baya ga rasa rayukan da aka samu, harin
jirgin yakin na ranar Laraba ya rusa gidaje da dam.
Sai dai wasu bayanai sun ce harin jirgin yakin
Najeriyar ya fada kan fararen hula ne a bisa kuskure, a lokacin da sojin ke
kokarin tarwatsa wata maboyar ‘yan ta’adda a wani yanki na karamar hukumar ta
Shiroro.
Kakakin Gamayyar Kungiyoyin fararen hula a Shiroro
Salis Mohammed Sabo, ya ce lamarin ya faru ne da safe a lokacin da yara ke
diban ruwa a wata rijiyar burtsatse da ke unguwar Kurebe, kamar yadda Daily
Trust ta ruwaito.
Zuwa lokacin wannan wallafa dai rundunar sojin
Najeriya ba ta ce komai kan faruwar al’amarin ba.
A cikin watan Satumban shekarar 2021, an taba samun
irin wannan kuskure, inda wani jirgin yakin Nijeriya ya kashe fararen hula 'ba
tare da niyya ba' a hare-haren da ya yi nufin kaiwa kan mayakan Boko Haram a
arewacin jihar Yobe.
Mazauna kauyen Buhari da ke gundumar Yunusari a kusa
da kan iyaka da Nijar, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa
mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu akalla 19 suka jikkata yayin hare-haren
jiragin yakin.
No comments