KAI DANSADAU! -Daga Jaafar Jaafar


Ban san yaushe Sanata Dansadau ya lalace haka ba. A lokacin Obasanjo yana daya daga cikin jajirtattun sanatocin da su ke fadawa shugaban kasa gaskiya, kuma su ke tsayawa tsayin daka akan kare hakkin jama’a.

Wallahi har yanzu ban manta wata rana a zamanin Obasanjo da limamin masallacin unguwar mu ya juyo bayan an idar Sallah ya ce a yiwa Sanata Dansadau addu’a saboda shugaban kasa ya sako shi a gaba saboda yana kare hakkin al’umma.

Abin takaici wai yau shi yake sauke limami akan ya fadawa shugaba gaskiya akan rayukan al’umma wanda da ba su ji ba, ba su gani ba da ake kashewa.

Post a Comment

0 Comments