Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kalamanka Taimakon ‘Yan Ta’adda Ne – Martanin Munguno Ga El-Rufa'i

Daga Ammar M. Rajab  Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguno, ya caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nas...



Daga Ammar M. Rajab 

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguno, ya caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan kalaman da ya yi kan harkokin tsaro, inda ya ce gwamnan yana fallasa bayanan sirri ne na tsaro kawai.

Babagana Munguno ya bayyana hakan ne a yau Alhamis jim kadan bayan taron majalisar tsaro da shugabannin hukumomin tsaro da ministoci, karkashin jagorancin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

Munguno ya soki El-Rufai da cewa ya cika yawan surutu, inda ya kara da cewa a fakaice kalaman na El-Rufai zai iya taimaka wa ‘yan ta’adda su sake sabon shiri, wanda hakan ka iya jefa rayukan wadanda aka yi garkuwa da su cikin hadari.

Munguno ya jaddada hakan ne a lokacin da yake amsa tambaya kan ikirarin El-Rufai na cewa sojoji sun gaza aikata wani abu duk da bayanan sirri da aka samu tun da wuri kan maboyar ‘yan bindigar da kuma shirin kai hare-haren na su.

“Maganar El-Rufa’i na iya kawo cikas ga sha’anin tsaro domin ‘yan fashin nan na iya komawa wasu wurare idan sun san cewa an gano maboyarsu a yanzu.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya yi magana akan hukumomin tsaro, yana mai cewa mun san su waye (‘yan bindigar), da kuma daga inda suka fito. Kuma, wannan yana da haɗari.

“Lokacin da ka fara yawan surutu, za ka yi ta barin zance. Yanzu, ko da ya ce mun san inda suke, shi kansa (wannan furucin) ya riga ya zama matsala. Domin da zarar ka furta, ko gaskiya ne ka fada ko karya ne, mutanen da suka yi garkuwa da mutanenka za su sauya wuri su koma wani waje. Abu ne mai sauki. Don haka wani lokacin yana da kyau a yi shiru kawai,"in ji Munguno.

No comments