Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Khalifa Muhammadu Sanusi Ya Fitar Da Mutane 59 Daga Gidan Yari A Kano

Gidauniyar Muhammadu Sanusi ll ta fitar da mutane 59 daga gidan yari, waɗanda su ka kasa biyan tara da kuma waɗanda a ka ɗaure s...Gidauniyar Muhammadu Sanusi ll ta fitar da mutane 59 daga gidan yari, waɗanda su ka kasa biyan tara da kuma waɗanda a ka ɗaure su sabo da basussuka da a ke binsu.

Da ya ke zantawa da manema labarai a yau Laraba, Shugaban gudanarwar gidauniyar, Mujtaba Abba, ya ce Khalifa ya biya kuɗaɗen tarar da na basukan mutane 59 ɗin,  kimanin  N16,820,370.

Abba ya yi bayani cewa Khalifa ya bada umarnin a biya wa ɗaurarru 26 kuɗaɗen tara da basuka a gidan yarin Kurmawa, wanda adadin kuɗin ya kama N4,466,500.

A cewar shugaban gudanarwar, Khalifa ya umarci a biya wa ɗaurarru 33 kuɗaɗen tara da basuka, wanda ya kai kimanin N11,380,770.

Ya ce gidauniyar ta fuskanci cewa s kwai jama'a da dama da laifukan su basu taka kara sun karya ba, inda ya ƙara da cewa yawancin lafiukan na rigimar bashi ne da sauran ƙananan laifuka.

Abba ya kuma yi kira ga al'umma masu halinsa su yi koyi da Khalifa Muhammadu Sanusi wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.

Ya kuma yi kira ga waɗanda su ka amfana da su zamto mutane na gari a cikin al'umma.

No comments