Gwamnan Imo, Hope Uzodinma Gwamnan Jihar Imo dake kudu maso gabashin Nijeriya, Hope Uzodinma ya ce sama da kashi 90 na mutanen dake dau...
![]() |
Gwamnan Imo, Hope Uzodinma |
Gwamnan Jihar Imo dake
kudu maso gabashin Nijeriya, Hope Uzodinma ya ce sama da kashi 90 na mutanen
dake daukar nauyin kashe kashen da ake samu a Yankin da kuma masu aikata kisan
Kiristoci ne.
Uzodinma ya ce abin
takaici ne yadda wadannan mutane ke watsi da koyarwar addinin Kirista wajen
daukar nauyi da kuma aikata kisan da ya mamaye yankin baki daya.
A sakon sa na bikin
Easter Gwamnan ya ce ya roki masu aikata irin wannan laifi da su mayar da wukar
su kube domin bai wa jihar damar ci gaba ganin yadda matsalar ta yi matukar
illa ga jama’a da kuma al’adun mutanen yankin.
Uzodinma ya ce sau da
yawa ya durkusa a kasa yana rokon masu aikata irin wadannan laifuffukan da su
daina kashe jama’a ba tare da sun aikata wani laifi ba, yayin da ya roke su da
su rungumi zaman lafiya da yafewa juna koda wane laifi aka musu, inda ya ce
shima ya nemi gafarar jama’a dangane da laifin da ya aikata musu wajen daukar
matakan gwamnatinsa da ba su musu dadi ba.
Gwamnan har wala yau ya
kuma bukaci duk wasu masu korafi da su bi matakan shari’a wajen gabatar da
korafin su.
No comments