Wata babbar kotu da ke zamanta a birnin Abuja na Nijeriya ya karbe kujerar Yakubu Dogara a majalisar wakilin kasar, kana ta umurci a cike gurbin da sauke dan majalisar ya samar.
Dogara, ne ke wakiltar mazabar Bogoro/Dass ta jihar Bauchi a majalisar wakilan tarayyar kasar, kuma ya taba zama shugaban majalisar daga shekarar 2015 zuwa 2019.
Alkalin kotun D.U. Okorowo, a wannan Juma’a, ya yanke hukuncin cewa canza sheka da Dogara ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin kasar kuskure ne, ganin cewa a karkashin jam’iyyar PDP aka zabe shi, saboda haka dole ya mika wannan kujera ga masu ita.
Dogara ya koma jam’iyar APC ne bayan da ya lashe zabe a PDP a shekarar 2019.
Tsamin dangantaka tsakaninsa da gwamnan jiharsa, Bala Mohammed na daya daga cikin dalilan da suka sa tsohon shugaban majalisar wakilan na Najeriya ya fice daga PDP, wadda ya shiga kasa da shekaru 5 da suka wuce.
0 Comments