Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ku Yafe Mana, Mun Gaza A Matsayinmu Na Shugabanni A Nijeriya -Elrufai

  Gwamnan Jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya Nasir El-Rufai ya nemi gafara al'umma bisa hare-haren da 'yan bindiga da ke ci...

 


Gwamnan Jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya Nasir El-Rufai ya nemi gafara al'umma bisa hare-haren da 'yan bindiga da ke ci gaba da salwantar da rayukan a yankunan Jihar Kaduna, musamman harin da aka kai wa jirgin kasa a ranar Alhamis.

Gwamnan, wanda cikin yanayi mai cike da damuwa ya ce haƙiƙanin gaskiya yana cikin matuƙar bakin ciki saboda rabonsa da ya yi bacci tun ranar Alhamis, kuma ba ya iya bacci ko da ya sha maganin bacci saboda tsananin tashin hankali.

El-Rufa'i ya yi waɗannan kalamai ne lokacin da ya je karamar hukumar Giwa domin bai wa al'umma hakuri da ta'azziya da jaje bisa abubuwan da ke faruwa.

Ya kai ziyarar ne ranar Alhamis ƙarƙashin rakiyar mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe da kuma wasu mukaraɓan gwamnatinsa.

A wani saƙon murya da masu taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai suka bai wa BBC, gwamnan ya ce hakkin shugabanci abu ne da wata rana zai tashi ya tsaya gaban Ubangiji domin ya yi bayyani kan abubuwan da ke faruwa da abubuwan da ya aiwatar.

"Hakkin shugabanci kamar yadda malamai da jagoran addinin kirista suka fada, abu ne wanda wata rana zan tsaya gaban Allah SWT in yi bayanin me na yi don tabbatar waɗannan abubuwa ba su faru ba.

"Ina tsoron wannan rana da zan tsaya a gaban Allah na fadi me na yi, me zan iya cewa mun yi? Saboda haka dole mu roƙi gafararku da afuwarku domin a gwamnatance mu muka kasa.

"Kuma al'umma da laifinku, amma zan zo kanku tukunna," in ji shi.

'Mun gaza'

Nasir El-Rufa'i ya ce babu shaka sun gaza a gwamnatance kuma ba su da wata hujja domin koma me ke faruwa ba su da bakin magana domin hakki ne da ya rataya a wuyansu su tashi tsaye su kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Gwamnan ya ce yana tsoron ranar gamuwarsa da Allah domin bayyani kan abubuwan da ya yi me zai iya cewa?

Sai dai ya ce su ma al'umma da nasu laifin amma sai dai kowane irin laifi suka yi hakki na gwamnati ne kuma laifi nasu ne.

"Ni a ganina wadannan matsaloli ba su da wahala amma a yanzu sun kasance masu wahala, shekara biyu zuwa uku da suka wuce, mun san inda 'yan ta'addan nan suke, mun san komai, akwai jiragen sama da ke ba mu bayanai da sojoji da 'yan sanda da jami'an tsaro na SSS.

"Ko waɗannan masu aikata wannan ta'addanci an san da su domin an kashe wasu a cikinsu a baya.

'An ƙi sauraran shawarata'

Gwamna Elrufai ya ce ganin tasanin tashin hankali da ƙaruwar hare-haren nan akwai lokacin da ya ba da shawarar cewa a shiga dazuzzuka da suka kasance maboyar wadannan 'yan ta'adda a ƙona su da kauyuka da dazukan baki daya.

Amma a cewar gwamnan bai samu goyon-baya ba saboda sojoji na cewa ai tun da ba yaƙi ake yi ba, idan har suka aikata hakan to nan gaba suna iya fuskatar matsala.

Gwamnan ya ce sojoji sun ba da hujjar cewa su tsoronsu shi ne nan gaba ana iya kama su idan suka bar aiki suka fita ƙetare a gurfanar da su kan laifin aikata laifukan yaƙi ko kashe fararen-hula.

Ya nuna takaicinsa kan yadda masu kashe waɗannan mutanen ba a ganin laifinsu, dai dai ya ce tun lokacin da kotu ta amince a ayyanasu a matsayin 'yan ta'adda suke ta matsa ƙaimi kan a ƙona dazukan, amma an ƙi sauraronsu.

'Zan gana da Shugaba Buhari'

Nasir Elrufa'i ya ce a gobe Juma'a zai gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kuma abubuwan da zai sake gabatar masa kenan domin jimi'an tsaro sun san komai suna kuma samun duk wasu bayanai na 'yan ta'addan.

Gwamnan ya ce hatta wayoyinsu da abubuwa da suke aikatawa duk ana sane, ba a yankin Giwa kadai ba, har da yankunan Birnin-Gwari da Dansadau da Chikun har jihar Neja.

'Mun san da hari kan jirgin kasa'

Gwamna Elrufa'i ya ce watanni biyu kenan da suka samu bayanan sirri daga jami'an tsaro cewa ana kitsa kai hari kan jirgin kasa.

Saboda duk zirga-zirga da abubuwan da 'yan bindiga ke aikatawa ana sani, har daga inda suke komai an sani, a cewarsa.

Hatta maganganunsu ta waya, kuma an rubuta wasiƙa zuwa ga hukumar kula da sufurin jiragen kasa kan cewa a daina zirga-zirga daren amma aka ƙi.

Ya ce wasikarsu na cewa a rinƙa komai da rana saboda zai fi tsaro da sauƙi wajen kai agaji idan wani abu ya faru. Zirga-zirgar jiragen kar su ke wuce 4 na yamma.

Ya ce yana sanar da hakan ne domin mutane sun san abin da ke faruwa saboda akwai waɗanda ya kamata suyi wasu ayyukan amma sun ƙi.

Sai dai gwamnan ya ce ba za su daina matsawa shugaban ƙasa da sojoji ba.

Me ya sa sojoji ba sa aiki?

Gwamnan ya ambato dalilai da dama daga ciki akwai rashin yawansu sannan wuraren da ake tashin hankali a kasar na da yawa.

Ya ce jihohi 32 sojoji ke aiki a yanzu, kuma yawan 'yan ta'adda na rinjayar sojoji, saboda sai mutum 100 su far wa sojoji da yawansu bai zarta 10 ba.

Sannan ba ko ina za a iya kai sojojin ba, akwai shigayen binciken na sojoji da 'yan ta'adda suka je suka kashe su da kwashe musu kayan aiki.

Sannan wata mastala in ji gwamnan ita ce ganin akwai mutanen da ke bai wa 'yan ta'adda bayanai, don haka daga bangaren al'umma akwai abubuwan da ake bukatar gyara.

Sannan sojoji ba su da irin makaman 'yan ta'adda ana fin ƙarfinsu.

Ya ce akwai bukatar karfafa jami'an tsaro da bankad mutanen da suke baiwa 'yan ta'adda bayanai kafin su kai hari.

-Rahoton BBC Hausa

No comments