Hukumar gudanarwar Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya da kuma Jami'ar Franco-British Interna...
Hukumar gudanarwar Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya da kuma Jami'ar Franco-British International University (FBIU) dake Kaduna, ta mika sakon yi ta'aziyyarta ga iyalan Marigayi Tahir Fadlallah wanda ya rasu da sanyin safiyar Juma'a, 29 ga watan Afrilun 2022 a birnin Beirut dake Lebanon. Ya rasu yana da shekaru 73.
Har ya zuwa rasuwarsa, Fadlallah ya kasance shugaban al’ummar kasar Lebanon a Kano, kuma shi ne mai Shahararren gidan Bakin nan na Tahir.
Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaba kuma wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, rasuwar Tahir Fadllah babban rashi ne ba kawai ga iyalansa da kuma al'ummar kasar Labanon a Nijeriya ba, har ma da daukacin al'ummar musulmin Nijeriya da ma duniya baki daya.
"Na yi matuÆ™ar kaduwa da jin labarin rasuwar Tahir Fadallah. Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakurensa, ya kuma ba shi Al-Jannah Firdausi,” inji Farfesa Adamu Gwarzo.
Farfesa Gwarzo ya bayyana Marigayin a matsayin dan kishin “Kano da Nijeriya" wanda ya jajirce wajen samar da ayyukan yi ga matasa a kamfanoninsa a lokacin rayuwarsa.
Ya labarta cewa Marigayi Fadallah yana cikin mutane 82 da gwamnatin jihar Kano ta karrama a shekarar 2017 saboda gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar.
"A Madadin Hukumar Gudanarwar Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ina son na mika sakon ta'aziyya ga iyalansa. Allah Madaukakin Sarki ya sanya shi a Al-Jannah Firdaus, ya kuma bai wa iyalai karfin gwuiwar jure wannan babban rashi.
Farfesa Adamu Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu a Afirka ya kuma jajantawa gwamnatocin Nijeriya da Lebanon da kuma jihar Kano bisa rasuwar Tahir Fadallah.
Ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya jikan Marigayin ya kuma ba shi Aljannar Firdaus da kuma bai wa iyalansa juriyar rashin da ba za aiya mayarwa ba.
Marigayin wanda ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar, tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Beirut na kasar Lebanon.
Allah ya jikansa da Rahama ya kuma gafarta masa, amin.
No comments