Daga Umar Idris Kaduna Murna da farin ciki da godiya ya turnuke jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa wato NSCDC da ke Wus...
Daga Umar Idris Kaduna
Murna da farin ciki da godiya ya turnuke jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa wato NSCDC da ke Wuse Zone 5 bayan gano macizai da dama a harabar ofishinsu dake Abujan.
An gano macizan ne sakamakon cizon da macijin ya yi ma wani ma’aikaci mai sanya na’u’rorin sadarwa, yayin da bukata ta kama shi, sai ya yanke shawarar yin amfani da bandakin dake harabar Hukumar ta NSCDC.
Macijin ya sare shi sau biyu a mazakutarsa, an garzaya da shi asibiti, amma daga baya danginsa suka dauke shi zuwa wurin masu maganin gargajiya.
Wasu jami’an da suka zanta da wakilinmu, sun bukaci a sakaya sunansu sun ce majizan sun bude filin kiwo ne a Hukumar ra NSCDC saboda rashin kulawa.
A ranar 29 ga Maris, 2022, hukumar rundunar ta NSCDC ta nemi taimakon wasu masu kama maciji, mai suna Dakta Ubale mai maciji cikin nasara sun kama macizai bayan gudanar da bincike na wasu lokuta
Da wakilinmu yake zantawa da shugaban ayarin masu kama macizan Dakta Ubale mai maciji shahararren masani akan maciji hagu da dama a nan gida Nigeriya da kasashen waje.
Dakta Ubale sai ya kada baki ya ce, "Dama bisa al'adar yankin garin Abuja da Gombe da yankin Jos da Kaltungo lokaci irin haka akan sami matsalar cizon maciji saboda zafi da duwatsu da suke a yankin.
"Bisa haka nake bada shawara jama'ar da suke yankin Abuja su kula da tsaftar gidajensu hakan zai taimaka masu kwarai daga matsalar maciji", inji shi.
Dakta Ubale ya tabbatar da samun nasarar kama manyan macizai fiye da 10 masu tsawon kafa 12 dukkansu masu illa ne ga rayuwar Dan Adam.
Dakta Ubale ya yi kira ga gwamnati akan sakaci da gwamnati ke yi akan matsalar cizon maciji a fadin kasa baki daya. Ya ce abin kunya ne idan maciji ya yi cizo yanzu sai a zagaya asibiti 10 ba allurar dake magance cizon maciji ya ce hakan bai kamata ba.
Karshe ya roki Gwamnatin Tarayya da ta farfado da wani tsari da ta kirkira lokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari na PTF ya ce akwai wani shiri mai suna 'Anti Snake Venoms Study Group NG/Uk' hadin guiwa ne da kasar Amurka wannan shiri ya taimaki 'yan Nijeriya da duniya baki daya don an tanadar wa tsarin komi kuma aikin ya biya bukata sosai.
Dakta Ubale ya ce mai zai hana shugaban kasa yasa kishinsa na son ci gaba ya dawo da wannan tsarin don magance matsalar cizon maciji a Nijeriya baki daya.
Ya zuwa yanzu jama'ar tsakiyar Abujan musamman ma wanda suka ga yadda lamarin ya wakana hankalinsu ya tashi matuka sai addu'a suke yi da roko ga ministan Abuja da ya taimaka ya gaiyyato Dakta Ubale yazo ya fesa masu wannan maganin don su samu kariya daga cizon maciji a gidajensu musamman wanda suke makwabtaka da dazukan dake Anguwannin tsakiyar Abujan.
No comments