Leadership Hausa ta labarto cewa; mahaifiyar mai kamfanin jaridar LEADERSHIP, Misis Eunice Ndanusa-Isaiah ta rasu. A cewar wata majiya daga ...
Leadership Hausa ta labarto cewa; mahaifiyar mai kamfanin jaridar LEADERSHIP, Misis Eunice Ndanusa-Isaiah ta rasu.
A cewar wata majiya daga dangi, Mista Joseph Nda-Isaiah, ya ce, ta rasu ne a Abuja da karfe 2:30 na daren Juma’a.
An haife ta a shekarar 1942 a tsohon garin Kabba da ke Arewacin Nijeriya, Mrs. Ndanusa-Isaiah ta rasu tana da shekaru 80 a duniya.
Ta taso a jihohin Kano da Kaduna da Neja kuma ta yi aure a 1961 da mijinta Mista Clement Ndanusa-Isaiah, fitaccen editan jaridar New Nigerian da Triumph.
Ana kiran ta da sunan “Mama Sam”, inkiya ce ta samo daga sunan danta na fari wanda ya kafa jaridar LEADERSHIP, Mista Sam Nda-Isaiah.
Sanarwar ta kara da cewa za a bayyana ranar jana’izarta nan bada jimawa ba.
No comments