Firaministan Pakistan Imran Khan ya rasa matsayinsa a Lahadin nan, bayan da ya sha kaye a zaben majalisar dokokin kasar. An dai sauke Im...
Firaministan Pakistan
Imran Khan ya rasa matsayinsa a Lahadin nan, bayan da ya sha kaye a zaben
majalisar dokokin kasar.
An dai sauke Imran Khan
ne, bayan shafe makwanni ana rikicin siyasa a kasar ta Pakistan.
Mukaddashin Kakakin majalisar
kasar Sardar Ayaz Sadiq ya ce 'yan majalisa 174 ne suka kada kuri'ar amincewa
da kudirin yankan kauna kan jagorancin tsohon Firaminista Imran Khan.
Babu wani Firaminista
da ya taba yin cikakken wa'adi a Pakistan, amma Khan shi ne na farko da ya rasa
mukaminsa ta hanyar kada kuri'ar rashin gamsuwa da gwamnatinsa.
Ba a dai fayyace
lokacin da majalisar Pakistan din za ta zabi sabon Firaministan kasar ba.
No comments